
Wata mata me suna Maman Zainab dake da kimanin shekaru 42 ta yanke jiki ta fadi ta rasu a yayin da ta halarci wajan tafsirin Azumin watan Ramadana.
Lamarin ya farune a Masallacin Gawu dake Abaji a babban birnin tarayya Abuja.
Wani mazaunin Unguwar me suna Ismail Bala ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust faruwar lamarin. Inda yace abin ya farune ranar Talata da misalin karfe 11:23 na safe.
Matar dai ta bar gida lafiya Qalau inda makwabtanta 3 suka rakata zuwa wajan Tafsirin saidai ana tsaka da Tafsirin, ta gayawa na kusa da ita cewa tana jin jiri. Ta mike zata tashi sai ta yanke jiki ta fadi.
Sauran matan sun dauke zuwa Asibiti a Gawu Babangida inda likitoci suka tabbatar da cewa ta mutu.
Likita ya bayyana hawan jini a matsayin abinda yayi sanadiyyar mutuwar ta.
Tuni aka yi jana’izarta kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.