
Dan jarida kuma tsohon editan jaridar Daily Times newspaper me suna Chief Tola Adeniyi ya soki kasancewar Sanata Godswill Akpabio a matsayin kakakin majalisar Dattijai.
Ya bayyana cewa, kamata yayi ace Sanata Akpabio na gidan yarine ba wai a majalisar dattijai ba.
Yace Akpabio da masu hali irin nasa kamata yayi ace suna gidan yari, ya kara da cewa ka je ka duba zarge-zargen da akewa Sanata Akpabio inda ake zargin ya ci kudi Biliyan 44 da biliyan 90 da dai sauransu.
Yace sannan kuma ga zargin lalata da sanata Natasha Akpoti ke masa.
Yace abin kunyane ace irin wadannan mutanen ne akewa jiniya ana yawo dasu a kan totunanmu.