
Rahotanni sun bayyana cewa, me taimakawa shugaban kasa kan yada labarai, Temitope Ajayi ya nemi a zartar da hukuncin kisa kan matashiya Ushie Uguamaye saboda sukar da tawa shugaba Bola Ahmad Tinubu.
Kafar peoplesgazette ce ta wallafa cewa Temitope Ajayi ya nemi a yankewa Ushie hukuncin kisa saboda yace a zartar mata hukunci mafi tsanani da hukumar bautar kasa ta NYSC ta tanadar.
Saidai a bayaninsa, Ajayi, ya bayyana cewa, shi ba haka yake nufi ba, an canja masa manufar bayaninsa ne dan cimma wani buri.
Yace abinda yake nufi da zartarwa da Ushie hukunci mafi tsanani a dokar NYSC shine a koreta daga aikin bautar kasar, yace shi a iya saninsa wannan ne hukunci mafi tsanani a dokar NYSC ba hukuncin kisa ba.
Lamarin Ushie ya dauki hankula sosai inda ciki hadda Atiku Abubakar, da Peter Obi da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty international sun saka baki a ciki.