Friday, April 25
Shadow

Gwamnatin Shugaban kasa, Donald Trump zata kulle gidan yada labarai na VOA

Rahotanni daga kasar Amurka sun bayyana cewa, shugaban kasar, Donald Trump yace zai kulle kafar yada labarai ta VOA.

Dalili kuwa shine ana zargin kafar da rashin nuna goyon baya ga shugaba Trump.

Shugaban VOA, Mike Abramowitz ya bayyana cewa, shi da ma’aikatansa, 1,300 duk an ce su tafi hutu kuma an dakatar da Albashinsu.

Ya bayyana cewa, wannan na zuwane a yayin da kasashe irin su Iran, China da Rasha ke yada labaran karya game da kasar ta Amurka.

Ana ganin dai wannan matakin kamar hanyace ta dakile aikin jarida da Shugaba Trump ya dauko.

Karanta Wannan  Kalli Cristiano Ronaldo tare da yariman Saudiyya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *