Thursday, March 20
Shadow

Dan Fim Din Kudu ya bayar da labarin yanda abokan aikinsa mata 3 suka masa fyàdè a yayin da suke wani otal daukar fim

Dan fim din kudu, Lanre Adediwura ya bayyana yanda wasu mata 3 abokan aikinsa suka masa fyade a yayin da yaje aikin daukar wani fim.

Yace da farko dai ya je wajan daukar fim dinne inda daga baya wata abokiyar aikinshi ta sameshi ta bayyana masa cewa, tana sonsa.

Yace a nan ya sanar da ita yana da aure amma tace ta ji ta gani.

Ya kara da cewa anan suka zauna suna buga karta ko wasan kati, da suka gama dare yayi, ya manta katin a hannunta.

Yace ta je dakin otal dinsa dan ta kai masa katin, inda anan ne ya ganta da abokanta biyu sun je su masa fyade.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Kalli Hotunan yanda Motar rusau ta bayyana a gidan Sarkin Nasarawa, inda Sarki Aminu Ado Bayero yake zaune yanzu haka

Ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda lamarin ya jawo cece-kuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *