
Har yanzu dai Sanata Natasha Akpoti bata saurara ba da yiwa kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio tonon silili.
A sabuwar hirar da ta yi da BBC Pidgin, Natasha tace majalisarsu kamar kungiyar tsafi take.
Tace kowane sanata na tsoron ya bayyana ra’ayin da ya sha banban da na kakakin majalisar saboda tsoron kada a saka masa ido.
Tace amma zargin da takewa Sanata Godswill Akpabio da gaskene, ta sake maimaita cewa akwai sanda suka je gidansa ya kama hannunta a gaban mijinta ya ja ya suna tafiya, tace ya rika murza mata hannu, tace kowace mace akawa haka tasan abinda ake nufi.
Tace hakanan akwai sanda ta manta ta tafi aiki da sauri bata dauki zoben alkawarinta na aure ba, tace Sanata Godswill Akpabio na ganinta sai yake ce mata yaya Natasha, naga baki saka zoben aurenki ba, mu shigo ne, tace a gaban kusan sanatoci 5 ne hakan ta faru.