Monday, March 24
Shadow

Rashin lantarki ya tilasta rufe babban filin jirgin sama na Landan

An rufe Heathrow da ke yammacin London – tashar jirgin sama mafi cunkuso a nahiyar Turai – sakamakon gobara da aka samu a kusa da cibiyar lantarki da ke kusa da filin jirgin saman.

Filin jirgin zai kasance a rufe har zuwa 12:00 na dare a yau Juma’a saboda matsalar lantarkin.

Wakilin BBC ya ce babu wata sanarwa kan lokacin da za a iya dawo da lantarkin a Heathrow kuma filin jirgin ba shi da wani zaɓi illa daukar matakin rufewa domin kare lafiyar fasinjoji da ma’aikatansa.

A bara fasinja miliyan 83 ne suka bi ta filin jirgin saman na Heathrow.

Karanta Wannan  Miji ya saki matarshi bayan da mawakin Amurka, Chris Brown ya sumbaceta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *