Wednesday, April 30
Shadow

Tsohuwar Ministar Jin Kai, Betta Edu da aka sauke saboda zargin karkatar da kudin Talakawa ta samu kyautar girmamawa a jami’ar Calabar

Tsohuwar minister Jin kai, Betta Edu wadda aka sauke saboda zargin karkatar da kudaden talakawa ta bayyana a wajan bikin cika shekaru 50 da kafuwar jami’ar Calabar dake jihar Cross-River.

Wani abin mamaki shine har kyautar karramawa aka baiwa ministar.

Da yawa sun yi mamakin ganin Ministar a bainar jama’a tana ta sha’aninta.

Kyautar da aka bata itace ta tallafawa al’umma da ta yi.

Daga cikin zarge-zargen kudaden da akawa ministar a baya sun hada da na Naira Miliyan N585 da kuma na Dala $640,000.

A baya dai tsohuwar ministar ta kuma shiryawa Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero shan ruwa a gidanta.

Karanta Wannan  An kubutar da daya daga cikin daliban da aka yi gàrkùwà dasu a jami'ar FUDMA jihar Katsina

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *