Wednesday, April 30
Shadow

‘Yansanda sun kama wanda suka fito zanga-zangar adawa da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu a jihar Yobe

A jihar Yobe dake Arewacin Najeriya, ‘yansanda sun kama shugaban kungiyar da suka fito zanga-zanga inda suke adawa da sabuwar dokar saka ido akan kafafen sada zumunta da ake son zartaswa.

Wanda aka kama din shine Abubakar Jawa wanda shine ya jagoranci masu zanga-zangar na jihar Yobe.

Bayan shi, akwai kuma mutane 4 da aka kama tare dashi wanda aka bayyana sunayensu kamar haka, Mohammed Kayeri Adam, Suleiman A. Gambo, Maimuna Abba, and Abubakar Jawa. 

Da aka Tuntubi kakakin ‘yansandan jihar, Dungus Abdulkarim ya musanta kamen inda yace su suna ma neman masu zanga-zangar ne dan basu kariya.

Karanta Wannan  Ku sake Tunani, Musulunci bai farlanta kulle makarantu ba a lokacin azumin watan Ramadana>>Ministar Ilimi, Suwaiba Ahmad ta jawo hankalin Gwamnonin Arewa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *