Friday, December 5
Shadow

PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba – Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce babbar jam’iyyar hamayyar ƙasar, PDP ba ta da kyakkyawan shiri da tsarin kayar da APC a zaɓen 2027 ba.

Yayin da yake jawabi a wata ganawa da manema labarai a Abuja, ranar Juma’a, tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce a yanayin da jam’iyyar PDP ke ciki a halin yanzu ba za a ce ta shirya wa zaɓen 2027, saboda rikicin shugabanci da jam’iyyar ke ciki.

”PDP ba ta shirya wa zaɓen 2027 ba, wannan a bayyane yake. Ga yadda suke tafiya a yanzu rikicin jagoranci na ci gaba da yi wa jam’iyyar tarnaƙi”, in ji shi.

A baya-bayan nan dai wasu daga jam’iyyun hamayyar ƙasar ciki har da PDp na ƙoƙarin samar da wata haɗaka domin tunkarar APC a 2027.

Karanta Wannan  'Yan Bìndìgà sun kai hari wani sansanin sojojin Najeriya dake jihar Zàmfara inda suka kori sojojin suka konashi, sojojin sun koka da rashin makamai

To sai dai da alama tafiyar na ci gaba da fuskantar tasgaro, saboda muradun wasu ƴansiyasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *