Friday, December 5
Shadow

An sanar da ranar da za a binne Fafaroma

An sanar da ranar da za a binne Fafaroma.

Fadar Vatican ta tabbatar da cewa za a yi jana’izar marigayi, Fafaroma Francis da ƙarfe 8 na safe agogon GMT, a ranar Asabar mai zuwa.

Hakan na zuwa ne yayin da fadar ta fitar da bidiyon da ke nuna mamacin kwance a cikin akwatin gawa, a cocin Casa Santa Marta da ke gidansa.

Bidiyon ya nuna gawar Fafaroma sanye da jar doguwar riga da hularsa ta fafaroma da kuma carbi a hannunsa.

A ranar Laraba ne za a mayar da gawar St Peter’s Basilica, inda za a ajiye shi domin mutane su yi masa bankwana har zuwa ranar Asabar da za a binne shi.

Karanta Wannan  Wallahi Daga Yau Na Koma Dan Izala Ganin Yadda Wasu 'Yàñ Daŕìķà Kè Mùŕña Da Rasuwàr Śhèik Iďŕis Duťsèn Tanshi Saboda Bambancin Akìda Duk Da Cewa Malami Ne Na Mùsùlùncì, Inji Abubakar Aliyu

Fafaroma Francis ya mutu ne a ranar Litinin yana da shekaru 88 a duniya, sakamakon bugun zuciya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *