Wednesday, May 21
Shadow

Matasan da suka goyi bayan Buhari na kiran tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito takara a 2027

Shugaban tsohuwar kungiyar goyon bayan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, Dr. Jibril Mustapha, ya yi kiran tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito takarar shugaban kasa a shekarar 2027.

A sanarwar da ya fitar a Legas, yace ya kamata tsohon shugaban kasar ya amsa kiraye-kirayen da ake masa domin shine Najeriya ke bukata a yanzu.

Yace Najeriya a yanzu tana bukatar shugaban kasa wanda zai hada kan kasar kuma Tsohon shugaba Goodluck Jonathan na da wannan abun da ake bukata.

Karanta Wannan  DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Kano ta gargaɗi matasa masu raka Sarkin Kano Aminu Ado Bayero gangami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *