Tuesday, May 20
Shadow

Ba a ga watan Zulki’ida ba a Najeriya – Fadar sarkin Musulmi

Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III ta ce ranar Talata ce 1 ga watan Zulki’ida na shekarar Hijira ta 1446.

Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jaririn watan ba a ranar Lahadi.

A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.

Hakan na nufin yau Litinin 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Atiku, Kwankwaso Da Peter Obi Sun Fara Tattaunawa Domin Hadewa Waje Daya Don Tunkarar Zaben 2027

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *