Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf Yace Ya Bada Umarnin Gyaran Dukkanin Hanyoyin Jihar Kano
Sakamakon karatowar lokacin damuna a yanzu haka gwamnan jihar Kano ya bayar da umarni ga hukumar dake kula da titunan jihar Kano akan a tabbata duk wani titi daya samu fashewa ko zaizayewa a cikin birnin Kano a tabbatar an gyara shi domin samun nutsuwa ga masu ababen hawa.
Wannan umarni da gwamnan ya bayar tuni ya fara aiki domin kuwa tuni hukumar ta KARMA ta fara aikin gyare-gyaren titunan da suka samu matsala.