
Gwamnatin jihar Akwa-Ibom ta bukaci ma’aikatan lafiya a jihar da su sha rantsuwa cewa ba zasu tsere ba idan ta dauki nauyinsu suka je suka yi karatu.
Shugaban ma’aikatan jihar, Elder Effiong Essien ne ya bayyana hakan inda yace zasu dauki ma’aikatan lafiya 600.
Yace wannan bukata dolece saboda a tabbatar da cewa ma’aikatan lafiyar sun gudanar da aiki daidai da yawan kudin karatun da aka kashe a kansu.