Saturday, December 13
Shadow

Na yi nadamar yin takara tare da Atiku saboda mutanen mu basu son dan Arewa>>Inji Ifeanyi Okowa wanda yawa Atiku Abubakar mataimaki a takarar shugaban kasa ta 2023 bayan ya koma APC daga PDP

Tsohon Gwamnan jihar Delta kuma dan takarar mataimakin shugaban kasa a shekarar 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa yayi dana sanin yin takarar shugaban kasa tare da Atiku.

Okowa ya bayyana hakane bayan da ya canja jam’iyya daga PDP zuwa APC.

Yace a wancan lokacin mutanensa sun nuna basa son yayi wannan takara a matsayin mataimakin Atiku amma duk da haka ya karba.

Yace ko a lokacin da suke yakin neman zabe ya lura cewa mutanen su basa son dan Arewa ya sake zama shugaban kasa amma ya ki kulasu.

Yace amma yanzu yana dana sani kan kin bin abinda mutanensa ke so.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo Da Duminsa: A karshe dai an baiwa Maiwushirya kyautar gida saboda 'YarGuda tace ba zata aureshi ba sai yana da gida

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *