Friday, December 5
Shadow

Karyace ‘Yan Arewa na zaune cikin aminci da walwala kuma suna mallakar gidaje a yankunan mu>>Inyamurai da Yarbawa suka mayarwa da Dattawan Arewa martani kan cewa ‘Yan Arewa basa mallakar Filaye da gidaje a Kudu

Kungiyoyin kare muradun Inyamurai da Yarbawa na Afenifere da Ohanaeze IndiIgbo sun mayarwa da kungiyar tuntuba ta Arewa, Arewa Consultative Forum martani kan zargin da ta yi na cewa ba’a bari ‘yan Arewa na mallakar Filaye da Gidaje a kudancin Najeriya, Musamman yankin Inyamurai.

Kungiyar Ohanaeze Indigbo ce ta fara yin martanin inda tace ‘yan Arewa da yawa na zaune lafiya a jihohin Inyamurai kuma wasunsu sun mallaki gidaje kuma babu me takura musu.

Kungiyar ta bakin mataimakin sakataren yada labaranta, Mazi Godwin Okenwa tace Inyamurai suna da karbar baki a duka jihohinsu.

Hakanan itama kungiyar kare muradin Yarbawa ta Afenifere tace wannan zargi ba gaskiya bane, kawai suna son saka siyasa ne a ciki.

Karanta Wannan  Sabbin Bayanai sun sake fitowa game da sojojin da ake zargin sun yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu Jhuyin mulki

Kungiyar ta yo maganane ta bakin kakakinta me suna Jare Ajayi inda yace irin wannan lamari ne yasa suke neman a baiwa kowane yanki damar cin gashin kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *