Friday, December 5
Shadow

Fiye da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025

Fiye da ɗalibai miliyan 1.5 sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar UTME ta 2025.

Daga cikin ɗalibai 1,955,069 da suka zauna jarrabawar UTME ta shekarar 2025, fiye da miliyan 1.5 daga cikinsu sun samu ƙasa da maki 200 a jarrabawar.

VANGUARD ta rawaito cewa rahoton kididdiga na sakamakon UTME na shekarar 2025 da Hukumar Jarrabawa ta JAMB ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa ɗalibai 420,415 kawai ne suka samu sama da maki 200 a wannan jarrabawar.

A yayin da ɗalibai 4,756 suka samu sama da maki 320, kimanin ɗalibai 7,658 ne suka samu tsakanin maki 300 da 319.

Karanta Wannan  Ji yanda Wata matar aure ta mauje mijinta da itace ya sheke a jihar Yobe

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *