Friday, December 5
Shadow

Ƴansanda na bincike kan mùtùwàr ƙananan yara biyar a cikin wata tsohuwar mota a Nasarawa

Rundunar ƴansandan jihar Nasarawa ta ce ta fara bincike kan mutuwar wasu ƙananan yara biyar a garin Agyaragu cikin ƙaramar hukumar Obi a jihar.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar SP Ramhan Nansel, ya fitar yau Litinin a birnin Lafia.

Sanarwar ta ce an gano gawawwakin yaran ne a cikin lalatacciyar motar da ke ajiye a gidan wani Mista Abu Agyeme.

Ta ce tuni kwamishinan ‘yan sandan jihar Nasarawa, Shetima Jauro-Mohammed ya umarci gudanar da cikakken bincike don tabbatar da haƙiƙanin abin da ya faru.

A ranar Lahadi da misalin ƙarfe 5:30 na yamma ne, wani magidanci ya kai rahoto ga ‘yansanda cewa an gano ƙananan yara kwance shame-shame ba sa motsi a cikin wata lalatacciyar mota da ke yashe a harabar wani gida.

Karanta Wannan  Kotu Ta Tura Mai Wushirya Zuwa Gidan Yari Bisa Kama Shi Da Laifin Wallafa Bidiyo Da Hotunan Fìtśàrà Da 'Yàŕ Wadà

Yaran waɗanda shekarunsu suka kama daga shida zuwa goma, mata uku ne sai maza biyu kuma an tabbatar da rasuwarsu ne a asibitin Aro da ke garin Agyaragu sakamakon abin da ake zargi shaƙewar numfashi ce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *