Friday, December 5
Shadow

An Hango ‘yan bìndìgà 300 a kan babura dauke da muggan makamai suna tafiya daga Zamfara zuwa jihar Naija

Akalla mutane 300 da ake zargin ‘yan bindiga ne, dauke da muggan makamai Akan babura, an hango su suna ketare hanyar Kontagora zuwa Minna, tsakanin Kampanin Bobby da Wamba a Karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da rana tsaka, inda hakan ya sa direbobi da fasinjoji suka tsere domin kare rayukansu.

Wani ganau ya bayyana cewa, an yi imanin cewa ‘yan bindigar sun fito ne daga Jihar Zamfara, kuma suna tafiya cikin ‘yanci zuwa Karamar Hukumar Mashegu ba tare da gamuwa da jami’an tsaro ba.

Wani direba da ya shaida lamarin ya ce babu ko da jami’in tsaro guda daya a lokacin da lamarin ke faruwa.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: In banda Azzaluman Shuwagabanni da Allah ya jarrabi 'yan Najeriya dasu, kowane Dan Najeriya ya kamata ace Miloniya ne saboda Arzikin da Allah yawa kasar>>Inji Bature, George Galloway

Shugaban Karamar Hukumar Mariga, Abbas Kasuwa Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin da aka tuntube shi. Ya bayyana cewa an tura hadin gwiwar jami’an tsaro zuwa yankin domin kare al’umma.

Haka kuma ya bayyana cewa, wasu ‘yan sa kai guda biyu daga Wamba sun rasa rayukansu bayan fafatawa da ‘yan bindigar, yayin da wani guda kuma ke karbar magani a asibiti.

Rahotanni sun kara nuna cewa dakarun soji da ke sansanin Beri sun fara motsawa domin tunkarar miyagun.

An yi ƙoƙarin tuntubar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Wasiu Abiodun, bai yi nasara ba har zuwa lokacin da ake hada wannan rahoto.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon yanda Uwargida ta hau amarya da duka bayan da amaryar ta je gaisheta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *