Friday, April 10
Shadow

Gwamna Zulum ya hana sayar da giya a jihar Borno

Gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya bayar da umarnin haramta sayar da barasa ko kuma giya a Maiduguri babban birnin jihar.

Zulum ya ce an ɗauki matakin ne saboda yadda ake samun ƙaruwar rikici tsakanin masu adawa da juna a ƙungiyoyin asiri, da karuwanci, da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi, da kuma ayyakan daba.

“Na ji daɗi da na ga sojoji da ƴansanda da sauran ɓanagarorin tsaro na nan, saboda mafi yawan wadan nan abubuwa… wasu ne daga cikin sojojin da aka sallama daga aiki, da sauran jami’an tsaro da aka kora, da ma wasu daga cikin jami’an soji da ke aiki, da ma fararen hula,” in ji Zulum.

Karanta Wannan  Bidiyo: Kalli yanda wata yar Najeriya ke sharbar kuka bayan da aka hanata shiga kasar Amurka bayan an ga abinda ta rubuta a shafinta na sada zumunta

“Babu wani sabon abu a wannan doka, idan har muna son mu tsaftace birnin Maiduguri, to babu wanda za a bari.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *