Mutane aun nutse a ruwa yayin da suka shiga jirgin ruwa dan tserewa harin ‘yan Bindiga a garin Gurmana dake karamar hukumar Shirori jihar Naija.
Yawanci idan maharan suka kai hari, mutane kan tsere zuwa wani tsibiri har sai kura ta lafa kamin su koma gidajensu.
Mutanen daai sun tserene ranar Laraba.
Saidai ranar Alhamis, yayin da suke dawowa daga kan tsibirin da suka samu mafaka, mutane 4 sun mutu, bayan da jirgin ruwan da suke ciki yayi hadari.