Tuesday, September 29
Shadow

An kama Barawo bayan da ya saci Keke Napep a masallaci a jihar Naija

Hukumar ‘yansandan jihar Naija sun yi nasarar kama wani barawon Keke Napep a jihar.

Kakakin ‘yansandan jihar, SP Wasiu Abiodun ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace lamarin ya farune ranar 5 ga watan April.

Sunan Barawon da aka kama Abdulaziz Salisu kuma yayi satar ne yayin sallar Asuba a Dakwa.

Yace bayan ya saci Keke Napep din yayi yunkirin kaiwa wani me suna Abubakar Mohammed dan ya sayar masa dashi.

Yace ana tsaka da sallah ne Abdulaziz ya fita ya sace Keke Napep din amma sai ‘yansanda suka kamashi a gadar Maje inda ya amsa cewa satota yayi.

Karanta Wannan  Ana ta kiran a kama wasu matasa da suka fito Zàngà-zàngà suna nuna cewa shugaba Tinubu na da hannu a matsalar tsaro

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *