Friday, December 5
Shadow

Hajj 2025: Maniyyata fiye da 2000 sun tashi zuwa ƙasa mai tsarki

Hukumar alhazan Najeriya ta ce ya zuwa ranar misalin ƙarfe 8:02 ta yi jigilar maniyyata 2,006 zuwa ƙasa mai tsarki.

Hukumar ta bayyana a shafinta na X cewa jirgin MaxAir ya tashi daga birnin Bauchi zuwa Madina, inda ya kwashi maniyyata 384 da kuma jami’i guda ɗaya.

Wannan dai shi ne cikamakin jirgi na biyar da suka yi jigilar maniyyatan daga ranar da aka ƙaddamar da jigilar wato ranar Juma’a.

Karanta Wannan  'Yan Bindiga sun kai hari Anka sun yi Gàrkùwà da mata 9

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *