Saturday, December 13
Shadow

Ba ‘yan Bindiga bane mune: Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Jirgin samansu da aka gani a daji

Hukumar ‘yansandan Najeriya ta yi karin haske kan Bidiyon da ya yadu sosai a kafafen sada zumunta inda aka ga jirgin samansu yana sauka da tashi a tsakanin wasu masu rike da makamai.

An yi zargin cewa jirgin ya je kaiwa ‘yan Bindiga kayan abinci da sauran kayan aiki ne.

Saidai a sanarwar da ta fitar ta shafinta na sada zumunta, Hukumar ‘yansandan tace ba ‘yan Bindiga bane aka gani a cikin Bidiyon ba. ‘Yansanda ne dake aikin samar da tsaro a dajin Obajana na jihar Kogi.

Hukumar tace a daina dogaro da bayanan da basu fito daga bakin hukumomin tsaro ba dan gujema labarin karya.

Karanta Wannan  Sanatan dake kan gaba wajan zuga shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kawo Khari Najeriya, Ted Cruz zai tsaya takarar shugaban Amurka a zaben 2028

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *