
Rikicin ‘yan matasan Arewa 89 da aka kai Matatar man Dangote dake Legas su yi aiki har yanzu bai kare ba.
Da farko dai hutudole ya kawo muku rahoton cewa, bayan kai matasan jihar Legas, an zargi cewa ‘yan Bindiga ne inda har ‘yansanda suka yi bincike kan lamarin suka gano cewa ba ‘yan Bindiga bane aiki aka kaisu su yi a matatar man fetur din ta Dangote daga jihar Katsina.
Saidai duk da wankesu, a yanzu kuma kungiyar kwadago ta jihar karkashin Wakilinta, Comrade Funmi Sessi sun ce basu yadda da kawo matasan ‘yan Arewa ba.
Yace wane irin aiki ne Wanda sai an dakko matasan Arewan zasu yi wanda matasan jihar Legas ba zasu iya yiba, yace kuma dokar Najeriya ta tanadi cewa, dole a baiwa mutanen da ke kusa da kamfanin Kaso 70 na ma’aikatan da za’a dauka in yaso sauran kaso 30 din ana iya kawo wasu daga waje.
Yace amma Dangote dama ya saba kawo ‘yan India su masa aiki a yayin da ake da wanda ke da kwarewa a Najeriya.
Yace dan haka suna kiran a mayar da wadannan matasa zuwa Arewa a kaisu wasu kamfanonin na Dangote dake Arewa idan ba haka ba zasu kira uwar kungiyar NLC ta kasa dan su dauki mataki.
Ya kara da cewa, kasancewar matasan masu samun kudi kadanne, zasu iya zama barazana ga jihar Legas.