
Rahotanni da hutudole ke samu na cewa, Peter Obi wanda dan takarar shugaban kasa ne a shekarar 2023 ya mince ya zama mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2027.
Rahotan wanda kafar jaridar Punchng ta ruwaito yace an yi zaman tattaunawa tsakanin Atiku da Peter Obi a kasar Ingila wanda a canne aka cimma wannan matsaya.
Da farko dai Atiku ya gayawa Peter Obi cewa ya zama mataimakinsa shi kuma zai yi zango data ne kawai ya sauka, Peter Obi yace a bashi lokaci zai je yayi Shawara.
Saidai Rahotan yace Tuni Peter Obi ya amince da wannan tayi.
A shekarar 2019 dai Peter Obi da Atiku sun yi takara tare amma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kayar dasu.