Friday, December 5
Shadow

‘Yan Bìndìgà sun yi gàrkuwà da babban Basarake a Arewacin Najeriya

Wasu ƴanbidga sun kai hari garin Okoloke da ke ƙaramar hukumar Yagba ta yamma a jihar ta Kogi, inda suka kashe aƙalla mutum uku are da jikkata wasu da dama.

Maharan sun kuma yi garkuwa da babban basaraken al’ummar ta Okoloke, Pa Dada James Ogunyanda, a lokacin da ake tsaka da zaman fadanci, wanda bayanai suka tabbatar da cewa ba shi da cikakkiyar lafiya kuma yana daf da tafiya neman magani, kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito.

‘Yan bindigar sun kuma kashe ƴanbanga biyu da wani ma’aikacin kamfanin sadarwa da ke aikin gyaran ƙarfen samar da sabis a yankin.

Rahotanni sun ce ‘yan bangar na samar wa ma’aikacin sadarwar tsaro ne lokacin da maharan suka yi musu kwanton ɓauna inda suka buɗe musu wuta nan take.

Karanta Wannan  Kada wanda muka sake jin ya biya masu Gàrkùwà da mutane kudin fansa>>Me baiwa shugaban kasa shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu ya gargadi 'yan Najeriya

Hare-haren ‘yan bindiga dai na ci aba da ƙaruwa a baya-bayan nan musamman a jahohin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya da ma shiyar arewa maso gabashin Najeriya. Waɗanda ke kashe mutane da garkuwa da wasu domin neman kuɗin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *