
Rahotanni daga jihar Osun na cewa masu laifi 7 ne suka tsere daga gidan gyara hali na Ilesa dake jihar a yayin da ake tsaka da ruwan sama.
Kakakin Hukumar kula da gidajen gyara hali na kasa, Abubakar Umar yace lamarin ya farune da dukudukun ranar Talata.
Yace tuni shugaban hukumar, Sylvester Nwakuche ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.