
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya zargi wasu jami’an sojoji da ƴan siyasa da kasancewa masu bai wa ƴan ta’addan Bòkò Hàràm bayanai da kuma hada kai da su.
Daily Trust ta rawaito cewa yayin wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Breakfast Central’ na tashar News Central, Zulum ya sha alwashin daukar saka kafar wando ɗaya da duk wanda ke kokarin kawo cikas ga kokarin gwamnatinsa na yaki da ta’addanci a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa za ta karfafa aikin leken asiri domin shawo kan ’yan ta’addan da masu taimaka musu.
Ya ce: “Muna da masu bayar da bayanai da masu hada kai da su a cikin Sojojin Najeriya, cikin ’yan siyasa da kuma a cikin al’umma.
“Abin da za mu yi shi ne mu karfafa aikin leken asiri kuma mu dauki mataki mai tsauri a kansu.
“Mu cire tsarin kwangila mara amfani. A cikin watanni shida za mu iya kawo karshen wannan hauka. Bai kamata mu sanya siyasa a cikin batun rashin tsaro ba.
“Ta’addanci ba zai kare da amfani da karfi kawai ba, dole ne mu tabbatar da cewa mun dauki matakan da ba na soja ba. Abin da nake nufi da hakan shi ne daukar matakan zamantakewa, siyasa da tattalin arziki dangane da wannan rikici.
“Bari in fada muku wani abu mai muhimmanci, ta’addanci ba zai kare da matakan ladabtarwa kadai ba. Daga cikin wadanda suka kai 300,000 ko fiye da suka tuba, ba zan ce babu wasu kadan da za su koma daji ba.”