Friday, December 5
Shadow

Bankin Duniya yace rabin mutanen Najeriya watau mutane sama da Miliyan 100 sun fada Talauci tsamo-tsamo

Bankin Duniya yace kusan rabin ‘yan Najeriya sun fada cikin talauci tsamo-tsamo saboda tsadar rayuwa dake karuwa akasar.

Sanarwar da bankin ya fitar yace kaso 46 na ‘yan Najeriya watau mutane Miliyan 107 sun fada cikin talauci inda suke rayuwa a kasa da Dala $2.15 a kullun.

Bankin yace ma’aikata basa samun rayuwa me kyau saboda Albashinsu baya kai musu yanda ya kamata.

A baya dai bankin yace akwai Talauci sosai a tsakanin kauyawan Najeriya.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Ba kowane hadisi ake yadda dashi ba>>Sheikh Dr. Ahmad Gumi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *