Friday, December 5
Shadow

Hotunan kananan yara da nake gani suna wahala a Gàzà akwai ban tausai, ina kira gareka da a kawo karshen wannan yàkì>>Shugaban Amurka Donald Trump ya sake yiwa Benjamin Netanyahu magana

Rahotanni daga fadar shugaban kasar Amurka, White House na cewa, shugaban Amurka, Donald Trump ya sake yin kira ga Firaiministan Israyla Benjamin Netanyahu da a kawo karshen yakin da suke yi da kungiyar Hàmàs.

Trump yace ya damu da hotunan da ya gani na yara suna shan wahala a Gaza yace abin akwai ban tausai.

Yace a yi sulhu sannan a saki wadanda aka yi garkuwa dasu sannan a kawo karshen yakin.

Jaridar Axios ta kasar Amurka tace wasu majiyoyi biyu sun shaida mata hakan daga fadar ta White House.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya ta fara gyaran manyan Tituna a duk fadin Najeriya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *