Friday, December 5
Shadow

Hatsarin ababen hawa ya kàshè mutum 1,593 a Najeriya cikin wata uku

Hukumar Kiyaye Aukuwar Haɗurra ta Najeriya, (FRSC) ta ce kimanin mutum 1,593 ne suka mutu sakamakon haɗurra a cikin wata ukun farko na shekarar 2025.

Cikin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna samun ƙaruwar munanan haɗurran da suka haddasa rasa rayuka da raunuka.

Hukumar ta bayar da rahoton cewa an samu haɗurra 2,650 a faɗin Najeriya daga watan Janairu zuwa Maris.

To sai dai bisa ga alƙaluman an samu raguwar yawan haɗuran idan aka kwatanta da daidai wannan loacin a 2024.

Haɗurran ababen hawa na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da asarar rayuka a Najeriya, wani abu da masana ke alaƙantawa da rashin kyawun titunan ƙasar, da kuma tuƙin ganganci daga ɓangaren direbobi.

Karanta Wannan  El-Rufai da Peter Obi Sun Tattauna a Gefen Taron Cambridge Africa Together a Birtaniya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *