
Kamfanin man fetur na ƙasa NNPC ya sanar da rufe Matatar mai ta Fatakwal a hukumance.
A wata sanarwa da ya fitar a Asabar din nan kamfanin na NNPC ya ce za a rufe matatar na tsawon wata ɗaya domin gudanar da wasu gyare gyare.
A cewar babban jami’in sadarwa na kamfanin na NNPC, Olufemi Soneye, ya ce rufewar ta fara aiki ne daga yau Asabar 24 ga watan Mayu.