Friday, December 5
Shadow

Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja

Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja.

…jama’a mu yada (sharing) wannan sako domin amfanar sauran jama’a

1) Allah Ya yi rantsuwa da su a cikin alQurani. Qur’an 89:2.

2) Sune Ayyamun Ma’alumat da Allah ya umurci ayi ambaton sa a ciki a suratul Hajj Qur’an 22: 28.

3) Aiki a cikin su yafi falala da lada da soyuwa ga Allah akan duk sauran kwanakin shekara. Bukhari no.926.

4) Ana so a yawaita Subhanallah, Walhamdulilllah, wallahu Akbar wa Lailaha illallah da karatun al-Qurani. Bukhari ya ruwaito.

5) Ana so a bayyana ambaton Allah a ciki domin a tunawa wanda yamanta. Abdullahi Ibn Umar da Abu-Hurairah sun kasance suna shiga kasuwa suna kabbara jamaa na kabbara da kabbarar su. Bukhari ya ruwaito .

Karanta Wannan  Ku zabeni, na yi Alkawarin wa'adi daya kawai zan yi in sauka>>Peter Obi

6) Aikin Hajji yana cikin Ayukka mafi falala a cikin wadanna kwanaki.

7) Annabi S.A.W ya kasance yana azumin kwanaki tara na farkon Zulhijja. Ahmad da Abu-Dawud da Nasai suka ruwaito . Albani ya inganta a Sahihi Sunani Abi-Dawud 2106.

8) Azumin ranar Arafah yana kankare zunuban shekarar da ta wuce da wadda za ta zo. Muslim 1162.

9) Idan kwanakin goma suka shigo wanda keda niyyar layya ba zai cire gashi ko kumba a jikin sa ba. Muslim ya ruwaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *