
Rundunar ƴansandan Najeriya ta samu nasarar hada matashiyar ƴar gwagwarmayan nan, Hamdiyya Shareef da mahaifan ta a Sakkwato bayan batan da ta yi a ranar Laraba.
Hamdiyya, wadda ta shahara wajen fafutukar ilimin ‘yan mata da kare hakkin matasa, ta bace a wani hali da ba a san ainihin dalilinsa ba, lamarin da ya tayar da hankulan mahaifan ta da dangin ta da masu goyon bayanta.
A cewar Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Sokoto, hadin gwiwa da hanzarin tattara bayanan sirri ne suka taimaka wajen gano inda take cikin koshin lafiya. Kakakin rundunar ya yaba wa ‘yan kasa bisa hadin kan da suka bayar tare da jaddada kudirin rundunar na kare duk wani dan Najeriya, musamman matasa masu rauni.
‘Yan uwanta, cike da hawaye da farin ciki, sun bayyana godiya ga ‘yan sanda da duk wanda ya tsaya musu a lokacin wannan jarrabawa.
Hamdiyya, wadda take bayyane cikin jin dadin samun ‘yanci, ta kara jaddada aniyarta ta ci gaba da gwagwarmaya, tana mai cewa wannan kwarewa da ta samu ta kara mata karfin gwiwa wajen kare hakkin marasa karfi.