
Hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta kulle matan gine-gine a birnin saboda rashin biyan kudaden haraji da ake binsu.
Wasu daga cikin manyan gine-ginen da aka kulle sun hada da:
Babban Ofishin Jam’iyyar PDP na kasa.
Ofishin hukumar tattara Haraji na kasa, FIRS dake Zone 5.
Ofishin Access Bank dake Wuse.
Da ofishin al’adun kasar China dake Zone 5.
Da gidan man Total dake Zone 5.
Da dai sauransu.