Friday, June 26
Shadow

Tsare-tsaren Gwamnatin Tinubu ya jefa Mutanen Najeriya cikin matsanancin Talauci>>Inji Janar Buratai

Tsohon shugaban sojojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta jefa ‘yan Najeriya cikin matsin talauci.

Ya bayyana hakane a wajan taron zagayowar ranar haihuwar tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi.

Yace gwamnatocin baya a hankali suka rika jefa ‘yan Najeriya cikin talauci amma Gwamnatin Tinubu, Lokaci guda ta jefa mutane saboda tsare-tsaren ta data gudanar masu tsauri.

Saidai yayi fatan nan da shekaru biyu masu zuwa a samu saukin rayuwa wanda yace idan ba haka ba, akwai matsala.

Karanta Wannan  Duk macen data san tana bin maza, yanzu an kawo sabon inji me gano maza nawa ta yi ma'amala dasu>>Murja Kunya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *