Friday, December 5
Shadow

Ku Godewa Allah: Rababa muke sayar muku da man fetur idan aka kwatanta da farashin man fetur din a sauran kasashen Africa>>Dangote ya gayawa ‘yan Najeriya

Babban Attajirin Najeriya wanda ya mallaki matatar man fetur mafi girma a Nahiyar Africa, Aliko Dangote yacewa ‘yan Najeriya suna cikin Alheri da sa’a dan kuwa suna sayen man fetur a farashi kasa da wanda sauran kasashen Africa ke saye.

Dangote yace farashin man fetur a Najeriya yana ana sayar dashi ne kaso 55 cikin 100 kasa da farashin da ake sayarwa a sauran kasashe.

Watau ‘yan Najeriya na siyan man fetur din a farashib kaso 45 cikin 100 idan aka kwatanta da sauran kasashen Africa.

Dangote yace kuma matatar mansa ta taimaka wajan rage farashin man fetur din a Najeriya daya tsaya a farashin tsakanin Naira 815 zuwa Naira 820 akan kowace lita.

Karanta Wannan  Yan Nigeria Basu iya Tattali Ba Amma N8,000 zata iya canza rayuwar matashi Wanda yasan meya keyi - Inji Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima

Dangote ya bayyana hakanne a yayin da shugaban Kungiyar ECOWAS, Dr Omar Touray da tawagarsa suka kai mai ziyara matatar tasa.

Yace za’a samu ci gaba sosai idan kasashen Africa suka karfafa kasuwanci a tsakaninsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *