
Kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta gargadi Najeriya kan ci gaba da ciwo bashi duk da yanda tattalin arzikin kasar ya tabarbare.
Hakan na zuwane yayin da Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ke shirin cin bashin da ya kai kusan Dala Biliyan $26.
Kungiyar tace kusan kaso 60 na kasafin kudi da gwanatin Tinubu ke dashi da bashi take kokarin aiwatar dashi inda tace hakan ya sabawa Alkawarin Gwamnatin Tinubu din na kaucewa bashi da mayar da hankali wajan jawo masu zuba hannun jari a Najeriya.
Kungiyar tace karuwar bashin Najeriya abu ne me hadarin gaske.
Sannan tace tana bayar da shawarar a mayar da hankali wajan samun kudi ta cikin gida da fadada hanyoyin kudin shigar Gwamnati ya fi a mayar da hankali wajan yawaita ciwo bashi.
Kungiyar tace duk da yawaitar bashin da Najeriya ke ciyowa amma yawan kudin shigarta bai karu ba.