
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, shine kashin bayan nasarar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi nasarar zama shugaban kasa a shekarar 2023.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta goyon bayan shugaba Tinubun a zaben shekarar 2027.
Saidai hakan baiwa jam’iyyun adawa dadi ba inda suke ta sukarsa. Jam’iyyun da suka soki Wike kan bayyana ci gaba da goyon bayan shugaban kasa Bola Tinubu sun hada da NNPC, PDP, CUPP.
Wike ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Wike yace bai aikata laifin yiwa jam’iyyarsa ta PDP zagon kasa ba inda ya kalubalanci jam’iyyar da cewa idan kuma ya aikata laifin to su dakatar dashi.
Saidai mataimakin shugaban matasa na jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor ya gayawa ‘yan Najeriya cewa, su yi watsi da kalaman na Wike inda yace kwanannan jam’iyyar zata san yanda zata yi dashi.
Jam’iyyar NNPP kuwa cewa ta yi za’a kayar da Tinubu a shekarar 2027 duk da goyon bayan da Wike ke bashi.
Shi kuwa wakilin CUPP, Mark Adebayo cewa yayi, Wike yaron shugaba Tinubu ne dake kokarin tarwatsa jam’iyyun Adawa.