
Rahotanni sun ce wani dan Bindiga me suna Dan Sadiya ya bayyana inda aka bayyana shi da cewa yafi Bello Tùrji illa.
Rahoton yace ya jagoranci kai hare-hare a jihar Zamfara wanda suka yi sanadiyyar kashe fararen hula da kuma kona kauyuka.
A cikin wasu Bidiyon da ya saki an ga ya nuna motar APC ta sojojin Najeriya da ya kwace wadda ake amfani da ita ana harbo jirgin sama.
An yi kira ga jami’an tsaro da su gaggauta daukar mataki akansa.
Ko kuna ganin wane mataki ya kamata a dauka akansa?