
”Yan kudancin Najeriya da yawa ne suke caccakar Gwamnatin jihar Kano bayan da ta ayyana kusan sati biyu a matsayin hutun sallah.
Gwamnatin jihar Kano ta sanar kwanaki 12 a matsayin hutun Sallah Babbah ga makarantu.
A arewa wannan ba sabon abu bane musamman lura da yanda ake dadewa a Kano ana bukukuwan sallah da ziyarar ‘yan uwa.
Saidai ‘yan Kudun a kafafen sada zumunta sun ta caccakar gwamnatin jihar Kanon suna dariya akai.