
Kasashen Larabawa sun roki shugaban Amurka, Donald Trump da ya saka Kungiyar ‘yan uwa Musulmi ta Muslim Brotherhood cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda.
Sun bayyana masa hakanne a yayin ziyarar da ya kai kasashen Larabawan a kwanakin da suka gabata.
Kasashen Larabawan da yawa ne dai tuni suka Haramta ayyukan kungiyar ta ‘yan uwa musulmi.
Tuni dai majalisar kasar Amurka ta fara muhawara dan saka kungiyar ta ‘yan uwa musulmi cikin jerin kungiyoyin ta’addanci a Duniya.