
Me kudin Duniya, Bill Gates ya bayyana cewa kudin da ake warewa bangaren lafiya a Najeriya sun yi kadan.
Yace sam kasafin kuin da ake warewa Najeriya ba zai iya magance matsalar rashin lafiyar da ake fama da ita ba a kasar.
Yace kasafin kudin Najeriya zai fuskanci tangarda musaman shekara me zuwa saboda babu kudin tallafin da aka saba bayarwa.
Bill Gates ya bayyana hakan ne ga manema labarai a yayin ganawar da yayi dasu a Legas.
Ya ce, Karancin kudin da bangaren kula da lafiyar Najeriya ke fama dashi shine yasa kasar ke kan gaba wajan yawan mutuwar mata masu ciki da jarirai sabuwar haihuwa a Duniya.
Ya kara da cewa mafi yawancin haihuwar da ake yi musamman a Arewacin Najeriya, yawanci a gida ake haihuwa kuma ko da sauran da ake kaiwa Asibiti, akwai asibitocin da basa iya yiwa mata masu ciki aiki.
Yace dan haka suna kokarin samar da wasu kayan aiki da zasu kawo sauki wajan haihuwa ga mata.
Yace misali, kasar India taka zagayawa da kayan aiki cikin unguwanni ne inda akewa mata masu ciki aiki a gida, yace amma hakan akwai kashe kudi sosai.