
Hukumar Lafiya ta yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana cewa, kaso 72 na yaran da suka kammala makarantun Firamare a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa basu iya karatu ba.
Wakilin hukumar a jihar, Joseph Senesie ne ya bayyana hakan a ganawa da manema labarai inda yace yara da yawa ana hanasu samun ilimi yanda ya kamata.
Yace yara Miliyan 2 ne a yankin basa samun zuwa makaranta. Yace kuma kananan hukumomi 12 a jihohin Borno da Yobe sunce akwai yara da yawa da ba’awa allurar Rigakafi ba.
Yace a cikin yara 10, 3 ne kawai ake samun rijitar haihuwarsu a hukumance wanda hakan ke sa basa samun tallafin karatu, Abinci da sauransu.
Saidai ya jinjinawa Gwamnatin jihar Borno kan kokarin da take na samar da tallafi ga rayuwar yara.