
Rahotanni daga kasar Iran na cewa, kasar ta yiwa kasar Israyla kutse inda ta kwashi bayananta game da makamashin kare danginta.
Rahoton yace kasar Iran ta dauki hayar wasu ‘yan kasar Israelan aiki ne inda ta rika biyansu makudan kudade wanda suka rika bata bayanan sirri game da kasar ta Israela.
Iran ta sanar da cewa ta dade tana wannan shirin kuma ba yau ta yi nasara ba amma dai ta tsaya ne kamin ta tabbatar da takardun bayanan sirrin kasar Israelan sun zo hannunta kamin ta sanar da nasarar ta.
Kasar Israyla dai bata ce uffan ba kan lamarin.
Saidai wasu rahotanni sun ce an kama wasu mutane da ake zargin sun hada kai da kasar Iran a cikin kasar ta Israela.
A shekarun baya dai, kasar Israela itama tawa kasar Iran irin wannan kutse.