
Sojojin Najeriya sun bayyana cewa, Sun kaiwa Masu ikirarin Jìhàdì mummunan hari ta jirgin sama a kauyen Talala da kauyen Ajigin dake yankin Timbuktu a jihar Borno.
Hukumar sojojin tace ta lalata kayan amfanin maharan da yawa.
An kai harinne ranar Asabar, 7 ga watan Mayu da misalin karfe 5:30 p.m.
Hukumar tace ta kai harinne bayan samun bayanai cewa mayakan masu ikirarin Jihadi na taruwa dan kaiwa sojoji hari.
Hukumar tace harin ya tarwatsa maharan inda da yawa suka jikkata kuma shirinsu ya lalace.
Hukumar ta yi gargadin cewa, wannan gargadi ne cewa ko a inane makiyansu suke zasu kai musu hari su tarwatsa su.