Friday, December 5
Shadow

Matawalle ya yi wa Dauda Lawal tayin shiga APC

Karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal tayin shiga jam’iyyar APC mai mulki.

Ministan ya yi tayin ne ranar Asabar a garin mahaifarsa ta Maradun, lokacin da ya karɓi bakuncin dubban magoya bayansa da suka kai masa gaisuwar barka da sallah.

Matawalle wanda ya kasance tsohon gwamnan Zamfara, ya ce APC jam’iyya ce ta mutanen kirki da dattako, don haka ya shawarci Dauda Lawal ya shiga jam’iyyar.

Ministan ya ce maimakon gwamnan ya bi ta ɓarauniya hanya, gara ya fito fili ya bi hanyar da ta dace wajen shiga APC.

“Ba ni da matsala da gwamnan idan yana son shiga APC. Ya zo ya bi sahun masu yunkurin kawo ci gaba a ɓangaren tsaro da zaman lafiya da kuma ayyukan raya ƙasa,” in ji Matawalle.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon tsohon gwamnan jihar Kaduna, ya yin da yake jiran jirgi a Filin jirgin sama na Cairo, kasar Egypt domin shillawa zuwa Abuja

Ya kuma ce shugaba Bola Tinubu jagora ne na gari mai son kawo zaman lafiya a kodayaushe, inda ya mayar da hankali wajen ayyukan da za su kawo cigaba a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *