
Zanga-zangar adawa da korar baki ta barke a kasar Amurka, musamman birnin Los Angeles.
Zanga-zangar ta fara ne bayan da hukumar ICE wadda itace ke kula da shige da fici ta kasar ta kama wasu mutane ‘yan cirani 118 wanda cikinsu akwai ‘yan daba.
Zanga-zangar ta barke sosai inda aka rika lalata motoci ana konawa hadda na jami’an tsaro ana yanka musu tayoyin mota.
Lamarin ya kazance inda aka fara shiga shagunan mutane ana musu sata.
Sannan an lalata gine-ginen Gwamnati.
Shugaba Trump ya aika da jami’an tsaro da ake kira da National Guard zuwa Birnin na Los Angeles inda ya zargin Gwamna Gavin Newsom na California da kin daukar matakin da ya kamata kamar yanda yayi sakaci da gobare daji a kwanakin baya.
Saidai Gwamna Gavin Newsom yayi Allah wadai da wannan mataki.
A birnin New York ma an samu rahoton zanga-zangar amma bata kai mumin ta Birnin Los Angeles ba inda rahotanni suka ce an kama masu zanga-zangar 20.
Hakanan a birnin Glendale na jihar Arizona ma an samu rahoton wannan zanga-zangar.